Hukumar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce jami’an ofishinta na shiyyar Lagos Zonal Directorate 2 ne suka gudanar da samamen a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2026.
A cewar EFCC, an gudanar da samamen ne bayan samun bayanan sirri da kuma sa ido kan ayyukan da ake gudanarwa a wuraren.
Hukumar ta ce jami’anta sun kwato buhunan duwatsun lithium, wayoyin hannu guda 18, kwamfutocin tafi-da-gidanka guda huɗu, na’urorin karɓar siginar talabijin guda biyu, na’urar sarrafa talabijin da kuma motar dakon kaya kirar tirela.
EFCC ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.
Lithium na daga cikin muhimman ma’adanai da ake amfani da su wajen ƙera batir, musamman waɗanda ake amfani da su a motocin lantarki da kuma wasu na’urorin lantarki.
