A cewar sanarwar hukumar da gidan talabijin na NTA ya wallafa, jami'an DSS sun gudanar da samamen ne a garin Dawakawa da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sokoto, bayan samun bayanan sirri kan wasu da ake zargi da safarar makamai.
Sanarwar ta bayyana cewa jami'an sun ƙwato bindigogin AK-47 guda 21, manyan bindigogin PKT guda huɗu da kuma harsasai 825.
Haka kuma, hukumar ta tabbatar da kama wata mata da ake zargi da hannu a safarar makaman.
DSS ta ce ƙara tsaurara matakan kama masu safarar makamai ya sa wasu ƙungiyoyin masu aikata laifuka sauya dabarunsu, ciki har da amfani da mata da dabbobi kamar raƙuma wajen jigilar makamai.
Hukumar ta kuma bayyana cewa ta kama mata 14 bisa zargin safarar makamai tsakanin watan Fabrairun 2025 da Nuwamban 2026 a sassa daban-daban na ƙasar.
Kama mata da ake zargi da safarar makamai a wasu jihohi
Wannan na zuwa ne bayan kama wata mata mai suna Hafsat Umar a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara ta Jihar Zamfara, inda ake zargin an same ta da gurneti guda 12 da bel ɗin harsasai guda biyu.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa ana zargin Hafsat ta yi tafiya zuwa Jihar Neja domin samo alburusai da za ta kai wa wani jagoran 'yan bindiga da ake zargi, mai suna Saidu Marafa, a Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.
Haka kuma, jami'an DSS sun kama wasu mata da ake zargi da safarar makamai a jihohin Nasarawa, Ebonyi, Taraba, Kaduna da Filato.
A watan da ya gabata, hukumar ta kama Aisha Mohammed a garin Keffi na Jihar Nasarawa, bisa zargin safarar harsasai 202 masu girman 7.62mm da ake amfani da su a bindigar AK-47.
A watan Satumban 2026, an kama Chika Aguzie da Blessing Nwamba a wurare daban-daban na Jihar Ebonyi bisa zargin samar da makamai da abubuwan fashewa ga kwamandojin ƙungiyar Eastern Security Network (ESN).
A yayin wannan samame, jami'an tsaro sun ƙwato na'urorin tayar da bama-bamai guda 14.
Haka kuma, a watan Agustan 2026, DSS ta kama Rabiatu Halidu a Ƙaramar Hukumar Katu ta Jihar Nasarawa, ɗauke da harsasai 501 masu girman 7.62mm.
A watan Fabrairun 2026 kuma, an kama Aisha Ibrahim a Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da harsasai 975.
Haka zalika, a watan Janairun 2026, jami'an hukumar sun kama Sakina Muhammad da Badariyya Abubakar a kan hanyar Wukari zuwa Jalingo a Jihar Taraba, inda ake zargin an same su da makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 da harsasai na manyan bindigogi.
Hukumar DSS ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin dakile safarar makamai da sauran hanyoyin samar da kayan aikin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da su.
