Rahotanni sun bayyana cewa wannan nasara ta samo asali ne daga ƙaruwar buƙatar kayayyakin da ke da alaƙa da fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) a kasuwannin duniya.
Haka kuma, fitar da kayayyakin China zuwa Amurka ya ƙaru da kusan kashi ɗaya bisa uku a watan Oktoba, duk da takaddamar kasuwanci da ke tsakanin manyan ƙasashen biyu.
Masana na ganin cewa ƙaruwar cinikayyar China da sauran ƙasashen duniya na iya ƙara haɓaka rarar cinikayyarta kafin ƙarshen shekarar.
Wannan na zuwa ne yayin da China ke ƙara ƙarfafa matsayinta a kasuwannin duniya, musamman wajen samar da kayayyakin fasaha da na zamani.
