Rahotannin sun nuna cewa mafi yawan waɗanda aka yanke wa hukuncin malaman addini ne.

Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Bahrain mai hedikwata a Birtaniya ta ce cikin waɗanda abin ya shafa har da fitaccen malamin Shi’a na ƙasar, Ayatollah Isa Qassim.

A nasa ɓangaren, ofishin masu gabatar da ƙara na Bahrain ya bayyana cewa an samu wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma da laifin kafa da gudanar da wata ƙungiyar ta’addanci da ake dangantawa da rundunar juyin juya halin Musulunci ta Iran.

Sai dai ofishin bai bayar da ƙarin bayani kan zarge-zargen ko waɗanda aka yanke wa hukuncin ba.

Bahrain ƙasa ce da iyalan sarauta masu bin mazhabar Sunna ke mulki, duk da cewa tana da ɗimbin al’ummar Musulmai ’yan Shi’a. Wasu daga cikinsu sun daɗe suna korafin cewa ana nuna musu wariya tare da tauye musu damarmaki a wasu fannoni na rayuwa.