Sakatare-Janar na ƙungiyar, Jassem Mohamed Albudaiwi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da GCC ta fitar ranar Juma'a.
Albudaiwi ya ce ƙungiyar ta yi maraba da haɗin kan ƙasashen duniya wajen amincewa da kudurin Kwamitin Tsaro mai lamba 2837, wanda ya buƙaci mayakan Houthi su dakatar da ƙara tsananta ayyukan soji da hare-hare, ciki har da waɗanda ke shafar fararen hula da muhimman ababen more rayuwa, kamar filayen jiragen sama da zirga-zirgar jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa.
Sakatare-Janar ɗin ya kuma yaba da ƙoƙarin Birtaniya wajen gabatar da daftarin kudurin, yana mai cewa matakin zai ƙarfafa matsayar ƙasashen duniya ta ƙin amincewa da hare-haren mayakan Houthi.
Ya yi kira da a mayar da kudurin zuwa wani tabbataccen mataki da zai kawo ƙarshen hare-haren, da kare rayukan fararen hula da muhimman wurare.
GCC Ta Sake Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwamnatin Yemen
Albudaiwi ya sake jaddada goyon bayan ƙungiyar GCC ga gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita, domin kare ikon ƙasar, haɗin kan al'ummarta, tsaro da zaman lafiyarta.
Yemen na cikin rikici tun shekarar 2014, lokacin da mayakan Houthi suka ƙwace iko da babban birnin ƙasar, Sanaa, da wasu yankuna.
Wannan mataki ya sa ƙawancen soji ƙarƙashin jagorancin Saudiyya shiga yaƙin a shekarar 2015, domin taimaka wa gwamnatin Yemen.
An samu ɗan sassaucin rikicin tun daga watan Afrilun 2022, amma sabon faɗan da ya ɓarke a watan Yulin 2026 ya kawo ƙarshen wannan yanayi na kwanciyar hankali.
A cewar rahotannin da aka danganta da Majalisar Ɗinkin Duniya, sabon faɗan ya yi sanadin mutuwar mutane ko jikkata wasu kimanin 12,000.
