Cibiyar ta bayyana cewa an samu ɗan lokaci na kwanciyar hankali a wasu yankuna, musamman a jihar Borno, lamarin da ke ƙara ƙarfafa sakamakon binciken da ta gudanar kan raguwar ayyukan ƙungiyar.

Rahoton ya kuma nuna cewa raguwar tashe-tashen hankulan na iya kasancewa da alaƙa da nasarorin da dakarun sojin Najeriya suka samu a yaƙi da ƙungiyar, musamman ganin cewa wannan raguwar ta fara ne tun kafin lokacin da aka bayar da rahoton cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Najeriya da wani ɓangare na Boko Haram.

Sakamakon binciken na ACLED ya nuna cewa an samu raguwar hare-hare da tashe-tashen hankula da ƙungiyar Boko Haram, wadda aka fi sani da Jama’atu Ahl al-Sunna li-Da’wa wa-l-Jihad, ke haddasawa a Najeriya a cikin rubu’o’i uku a jere na shekarar 2026.

Wannan yanayi ya zo ne a daidai lokacin da aka samu rahoton cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Najeriya da wani ɓangare na Boko Haram ƙarƙashin jagorancin Bakura Doro a watan Yuni.

An ce yarjejeniyar ta biyo bayan tattaunawar da ta kai ga sakin fararen hula 360 da aka yi garkuwa da su a yankin Ngoshe na jihar Borno.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin cimma wannan yarjejeniya, wadda kafar yaɗa labarai ta The New Humanitarian ta fara wallafawa a watan Satumba.

Wasu mutane uku da ke da alaƙa da mambobin Boko Haram, ciki har da wasu manyan shugabannin ƙungiyar, sun shaida wa kafar labaran cewa yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki tun watan Yuni, kuma ana sa ran za a tsawaita wa'adinta.

Kimanin watanni biyu bayan wallafa rahoton, rundunar sojin Najeriya ta sake musanta batun, tana mai cewa dakarunta na ci gaba da yaƙi da dukkan ƙungiyoyin ta'addanci a fagen daga.