Rahoton ayyukan rundunar da aka fitar a watan Nuwambar 2026 ya ce ta samu rahotannin hare-haren ’yan bindiga guda 168 da kuma ayyukan ta’addanci 51 a sassa daban-daban na ƙasar cikin makonni takwas.
Haka kuma, rahoton ya nuna cewa an samu rahotannin fashi da makami guda 165, rikicin ƙungiyoyin asiri 73 da kuma laifukan cin zarafin mata da jinsi guda 49 a cikin wannan lokaci.
Rundunar ta ce ta kama mutane 1,519 da ake zargi da aikata laifuka, tare da ƙwato bindigogi 191 da alburusai 3,873. Haka kuma, ta ƙwace motoci 117 da aka sace ko kuma ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifuka.
Bugu da ƙari, jami’an tsaro sun ceto mutane 255 da aka yi garkuwa da su, yayin da aka kashe mutane 56 da ake zargin ’yan bindiga ne a yayin samamen tsaro da aka gudanar a faɗin ƙasar, a cewar rahoton.
Rundunar ta bayyana cewa ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro bisa bayanan sirri da amfani da fasahohin zamani, tare da haɗin gwiwar rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, domin yaƙi da ta’addanci, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ƙungiyoyin asiri.
“A tsawon waɗannan watanni biyun, rundunar ’yan sandan Nijeriya ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro masu tsauri, bisa bayanan sirri da amfani da fasahohin zamani, tare da haɗin gwiwar rundunar soji da sauran abokan hulɗa a ɓangaren tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma ƙungiyoyin asiri a dukkan sassan ƙasar,” in ji rahoton.
Da take ƙarin haske kan halin da ake ciki na tsaro a Nijeriya, rundunar ta ce bayanan laifuka daga sassa daban-daban na ƙasar sun nuna cewa ana ci gaba da sanya ido tare da ɗaukar tsauraran matakan tsaro, musamman a yankunan da ke fuskantar barazanar rashin tsaro.
Rundunar ta danganta nasarorin da aka samu da jajircewa da sadaukarwar jami’anta, tare da jaddada ƙudurinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar.
“Waɗannan nasarori sun zama shaida ta jarumta, sadaukarwa da jajircewar jami’an rundunar ’yan sandan Nijeriya, waɗanda ke ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen sauke nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ɗora musu na kare rayuka da al’umma, tare da tabbatar da tsaron ƙasarmu, ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na ’Yan Sanda,” a cewar rahoton.
