Rahotanni sun ce matar ta yi ikirarin cewa wasu mutane sun yi garkuwa da ita tare da kai ta cikin daji, inda suka buƙaci a biya su naira miliyan 15 domin su sake ta.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar ne ya bayyana hakan a wani bidiyo da aka nuna matar tana amsa laifin da ake zarginta da aikatawa.
Mai magana da yawun rundunar ya ce an kai rahoton lamarin hedikwatar ’yan sanda ta Ogwashi-Uku a ranar 23 ga Oktoban 2026, lamarin da ya sa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya umarci sashen yaƙi da garkuwa da mutane da ke Obu-Luku, a Ƙaramar Hukumar Aniocha ta Kudu, da ya gudanar da bincike.
Ya ce jami’an sashen sun gudanar da binciken sirri, wanda ya gano yadda aka shirya lamarin tare da kai ga cafke matar.
A cikin bayanin da ta yi a bidiyon, matar ta amince cewa ita ce ta shirya sace kanta, sannan ta nemi ƙaninta ya tura mata kuɗin fansar.
“Ni na kitsa komai. Na kira ƙanina na sanar da shi cewa an yi garkuwa da ni lokacin da na fita sayen magani, kuma an kai ni cikin daji,” in ji matar.
Ta ce ta sanar da shi cewa waɗanda suka yi garkuwa da ita suna neman naira miliyan 15, kuma idan bai biya kuɗin ba, za su kashe ta.
“Aikin shaidan ne. Ina neman afuwa. Aikin shaidan ne,” in ji ta.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce za ta gurfanar da matar a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.
