Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a sace yaron.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa a ranar 8 ga Nuwamban 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na safe, mahaifin yaron mai suna Haruna Bala, mai shekaru 30, ya kai rahoton cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun shiga gidansa tare da yin garkuwa da ɗansa.

Sanarwar ta ce masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa naira 300,000, amma bayan tattaunawa da mahaifin yaron, sun rage kuɗin zuwa naira 30,000.

Rundunar ta ƙara da cewa bayan samun bayanan sirri da gudanar da bincike, jami'anta sun gano inda ake tsare da yaron a wani shago da ke ƙauyen Kunkumi, inda suka yi nasarar ceto shi tare da kama mutum biyu da ake zargi.

A ƙarshe, ’yan sandan sun tabbatar da cewa an ceto yaron cikin ƙoshin lafiya ba tare da ya samu rauni ba, kuma tuni aka miƙa shi ga iyalansa.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken yadda lamarin ya faru da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban shari'a.