Sean Duffy ya ce matsalar ta faru ne sakamakon lalacewar tsofaffin na’urorin sadarwa, yana mai yin watsi da zargin cewa an yi wa tsarin kutse ta intanet.
An soke tafiye-tafiyen jiragen sama da dama bayan da aka dakatar da zirga-zirgar na tsawon sama da sa’o’i huɗu. Sai dai harkokin sufuri sun fara komawa yadda suke a da.
A nasa ɓangaren, shugaban Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Amurka, Bryan Bedford, ya ce tsofaffin na’urorin sadarwa za su ci gaba da haddasa matsaloli matuƙar ba a sauya su da sababbi ba.
