Al-Burhan ya kuma yi kira da a samar da hanyoyin samun tallafin cikin sauri da sauƙi da kuma adalci, ba tare da sanya siyasa cikin tsarin raba kuɗaɗen ba.
Da yake jawabi a ranar Laraba, yayin zaman farko na taron shugabannin ƙasashe da gwamnatoci na COP31 da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya a birnin Antalya na ƙasar Turkiyya, Al-Burhan ya ce ya zama dole alƙawuran tallafin sauyin yanayi su zama kuɗaɗen da ƙasashe masu tasowa za su iya samu cikin sauƙi.
Ya buƙaci ƙasashen da suka ci gaba da su ƙara ƙoƙarinsu wajen ninka kuɗaɗen da suke warewa domin taimaka wa ƙasashe masu fama da illolin sauyin yanayi.
Haka kuma, ya yi kira ga gwamnatoci da su ɗauki matakan yaƙi da sauyin yanayi a matsayin wata dama ta bunƙasa ci gaba, zaman lafiya, tsaro da adalci.
Al-Burhan ya bayyana cewa Sudan na fuskantar barazanar ƙaruwar fari, ambaliyar ruwa, kwararowar hamada, lalacewar filaye da kuma ƙarancin ruwa.
Ya ce raguwar ayyukan noma da kiwon dabbobi na barazana ga samar da abinci da kuma hanyoyin samun abin dogaro ga al'ummar ƙasar.
Ya nemi a ba ƙasashen da suka fi fuskantar barazana fifiko
Al-Burhan ya ce halin da Sudan ke ciki ya ƙara tsananta matsalolin sauyin yanayi, musamman sakamakon lalacewar ababen more rayuwa, cibiyoyin gwamnati da ayyukan hidimar jama'a, tare da raunana ƙarfin al'umma wajen tunkarar waɗannan ƙalubale.
Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa bisa adalci, yana mai cewa dukkan ƙasashe suna da alhakin yaƙi da sauyin yanayi, sai dai nauyin da ke kansu ya kamata ya bambanta bisa ƙarfin tattalin arzikinsu da gudummawar da suke bayarwa wajen haddasa matsalar.
Ya kuma buƙaci a yi la'akari da yanayi da buƙatun ƙasashe masu tasowa, musamman ƙasashe mafi ƙarancin ci gaba da kuma waɗanda rikice-rikice suka shafa.
Idan za a iya tunawa, tun daga watan Afrilun 2023 ne aka fara yaƙi tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa rikicin ya tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu, tare da takaita samun ruwan sha mai tsafta, kiwon lafiya da matsuguni a sassa daban-daban na ƙasar.
