Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri, Funso Adebiyi, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar duba aikin da jami’an Ofishin Kula da Basussukan Ƙasa (DMO) da sauran jami’an gwamnati suka gudanar daga Jaji zuwa tashar jirgin ƙasa ta Kano.

Adebiyi ya ce tashar jirgin ƙasa ta Kano ta kusa kammaluwa, inda sanya allon sunan tashar ne kawai ya rage.

Ya bayyana cewa an kammala gyare-gyaren da aka buƙata bayan ziyarar duba aikin da ta gabata, ciki har da maye gurbin gilashin da ke wuraren da fasinjoji ke jira domin ƙara tsaro, da kuma sauya fitilun tashoshin zuwa waɗanda za su iya ɗaukar aƙalla shekaru uku kafin buƙatar sauya su.

Haka kuma, an samar da na’urorin ɗagawa domin sauƙaƙa ayyukan gyara, yayin da ake shirin horas da injiniyoyin Hukumar Jiragen Ƙasa ta Najeriya kan yadda za su gudanar da ayyukan tashoshin.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar na neman amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin gudanar da gwajin zirga-zirgar jirgin ƙasa na tsawon watanni uku daga Jaji zuwa Kano, wanda ka iya kasancewa kyauta ga fasinjoji.

A cewarsa, gwajin zai taimaka wajen tantance ingancin layin dogo da tsarin gudanar da zirga-zirgar jiragen ƙasa kafin fara jigilar fasinjoji ta kasuwanci.

Adebiyi ya kuma bayyana cewa gadar da za ta haɗa sauran ɓangaren aikin tsakanin Jaji da Kaduna ta kusa kammaluwa, yayin da ake ci gaba da faɗaɗa tashar jirgin ƙasa ta Kaduna domin ta iya karɓar ƙarin fasinjoji.

A nata ɓangaren, Darakta-Janar ta DMO, Patience Oniha, ta yaba da ingancin aikin tare da bayyana gamsuwarta da yadda aka gudanar da shi.

Adebiyi ya kuma ce aikin layin dogo daga Kano zuwa Kazaure, Daura da Katsina na ci gaba, duk da wasu ƙalubalen da suka shafi mallakar filaye.

Ya bayyana cewa layin dogon Kaduna zuwa Kano wani ɓangare ne na babban shirin gwamnatin Najeriya na haɗa manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a ƙasar ta hanyar sufurin jiragen ƙasa.