A wata tattaunawa da BBC Hausa, Gwamna Yusuf ya yi bayani dalla-dalla kan yadda dangantakarsa da matarsa ta samu tangarɗa. Zainab ɗiya ce ga marigayi ɗan'uwan tsohon gwamnan Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya a jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso.
A ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamba, Gwamna Abba ya furta wasu kalamai a yayin taron ƴan fansho da aka gudanar a babban ɗakin taro na gwamnatin jihar Kano.
Kalaman nasa sun biyo bayan raɗe-raɗin da ake yi kan saɓani tsakaninsa da matarsa, bayan rahoton jaridar Daily Nigerian cewa Zainab Kwankwaso ta shigar da ƙara a wata kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, tana neman a raba aurenta da gwamnan.
Lamarin ya haifar da muhawara saboda alaƙar siyasa da ke tsakanin gwamnan da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya kasance ubangidansa a siyasa.
Me ya haifar da rikicin?
Sanye da farar babbar riga da jar hula mai tambarin shugaban Najeriya, Bola Tinubu, Abba Kabir Yusuf ya ɗan ja lumfashi kafin ya fara amsa tambayar wakilin BBC kan kalaman da ya furta waɗanda ake zargin sun shafi iyalinsa.
"Irin wannan harka ta iyali abu ne mai matuƙar wahala," in ji Gwamna Yusuf.
Ya ci gaba da cewa: "Ita dai wannan mata, Zainab, ƴar wansa ce (Kwankwaso). Ya yi mata aure, amma auren nata bai daɗe ba. Daga nan Allah Ya haɗa mu muka yi aure kimanin shekara 20 da suka wuce, kuma muna da yara."
"Abubuwa da yawa sun faru, har ta kai ga aka kwashe kaya, sannan aka zo aka ɗauke ta daga gidana. Duk na yi haƙuri ban yi magana ba," kamar yadda Abba Kabir ya shaida wa BBC.
Gwamnan ya ce har ya shaida wa yaransu cewa Zainab za ta dawo gidansa.
"Kwatsam sai ga shi ya sa ta ɗirka ni a kotu, kotun ma a Abuja, ba a Kano ba," in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa lamarin "abu ne babu daɗi".
Gwamnan ya ce duk da ba zai bayyana wa duniya yadda aka bi wajen ɗauke matarsa daga gidansa ba, yana da shaidu da bayanai dalla-dalla kan yadda lamarin ya faru.
A cewarsa, bai kamata lamarin ya zama abin cece-ku-ce ba, domin irin waɗannan abubuwa na faruwa.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya yi magana kan lamarin a bainar jama'a, Gwamna Yusuf ya ce:
"Ai ba ni ne na siyasantar da abin ba. Kai yanzu idan aka yi maka haka, za ka ji daɗi?"
"A kwashe wa iyalinka kaya ba da sanin ka ba, a zo a ɗauke ta a garkuwa da ita ba da sanin ka ba, a tafi da ita gidan wani, ba da sanin ka ba, sannan kawai sai ka ji cewa ita ce ta kai ka ƙara kotu."
Gwamnan ya ce ana ci gaba da duba lamarin, kuma akwai yiwuwar a samu maslaha.
BBC Hausa ta ce za ta wallafa cikakkiyar hirar a shafinta na YouTube.
Wace ce Zainab Musa Kwankwaso?
Zainab Musa Kwankwaso tamkar ɗiya ce ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asalin sunanta Zainab Dahiru Musa, sai dai mahaifinta, wanda yaya ne ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya rasu tun da daɗewa.
A sanadiyyar haka ne Zainab ta taso a gidan Rabiu Musa Kwankwaso har zuwa lokacin da ya aurar da ita.
Ta auri gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a shekarar 2006, kuma aurensu ya shafe shekara 20, inda suke da ƴaƴa shida.
Ana ganin saɓani ya shiga cikin aurensu ne bayan doguwar taƙaddamar siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon jagoransa a siyasa, wanda kuma shi ne uba ga matarsa, Rabiu Musa Kwankwaso.
Rikicin ya fara ruruwa ne tun bayan da Abba Kabir ya zama gwamnan Kano a shekarar 2023.
A cewar rahoton jaridar Daily Nigerian, a tsakiyar watan Nuwamban 2026, Zainab ta shigar da ƙarar neman raba aurensu a wata kotu da ke Abuja, inda kotu ta miƙa wa Gwamna Abba sammaci.
Wane ne Abba Kabir Yusuf?
Abba Kabir Yusuf shi ne gwamnan jihar Kano, jiha mafi yawan al'umma da kuma hada-hadar kasuwanci a arewacin Najeriya.
Ya lashe zaɓen gwamna a shekarar 2023, bayan ya sha kaye a zaɓen shekarar 2019.
Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taka muhimmiyar rawa a nasarar Yusuf a zaɓen 2023, sai dai daga baya sun raba gari.
Komawar Yusuf jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ba tare da ubangidan nasa ba ta kawo ƙarshen gomman shekaru da mutanen biyu suka kwashe suna aiki tare.
Mutane da dama sun riƙa zargin gwamnan da yin butulci, sai dai a tattaunawarsa da BBC Hausa, Abba ya musanta hakan.
An haifi Abba Kabir Yusuf a ranar 5 ga watan Janairu, 1963, a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.
Ya kasance kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabiu Musa Kwankwaso.
Abba Gida-Gida ya yi takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019, amma bai samu nasara ba.
