An Lalata Makarantu Fiye da 1,400, An Kashe Malamai 2,295 a Arewa Maso Gabashin Najeriya
Gwamnatin Jihar Borno ta ce an lalata makarantu fiye da 1,400 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, yayin da aka kashe malamai 2,295, sakamakon rikicin ta’addanci da yankin ya kwashe shekaru yana fama da shi. Gwamnatin ta kuma ce kimanin yara miliyan uku ne ke buƙatar tallafin gaggawa a fannin ilimi, sakamakon tasirin rikicin da ya shafi yankin. Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ne ya bayyana hakan yayin da yake wakiltar Gwamna Babagana Umara Zulum a wani taron tattaunawa na ƙasa na kwanaki biyu kan illar rikici ga lafiyar ƙwaƙwalwar yara a Najeriya, wanda aka gudanar a Maid
