Sojojin Iran sun sanar da cewa sun kai hare-hare da jiragen sama marasa matuƙa (drones) kan wasu sansanonin sojojin Amurka da ke Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) .
A cewar sanarwar rundunar, an kai hare-haren kan sansanonin Dhafra da Manhad da ke UAE, yayin da aka kuma kai wasu hare-hare kan sansanin Sheikh Isa da ke Bahrain.
Iran ta ce hare-haren sun kasance ramuwar gayya ne kan hare-haren da jiragen yaƙin Amurka suka kai a baya.
Rahotanni na baya-bayan nan sun tabbatar da cewa Iran ta ƙara kai hare-hare kan wuraren da sojojin Amurka suke a wasu ƙasashen yankin, ciki har da Bahrain da Kuwait, bayan sabon zagaye na hare-haren Amurka da Iran.
Sa’o’i kaɗan kafin wannan sanarwa, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kuma sanar da kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke Kuwait da Jordan .
Lamarin na zuwa ne yayin da rikicin tsakanin Iran da Amurka ke ƙara tsananta, lamarin da ya janyo fargabar faɗaɗuwar rikicin zuwa sauran ƙasashen yankin.
