Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei , ya yi kira ga shugabannin ƙasashen Musulmi, musamman na Gabas ta Tsakiya da yankin Tekun Fasha, da su haɗa kai domin tunkarar abin da ya kira barazanar Amurka da Isra’ila .

Kamfanin Dillancin Labaran Iran, IRNA , ya ruwaito cewa Khamenei ya yi wannan kiran ne a wani saƙo da aka gabatar yayin taron Makon Haɗin Kan Musulunci .

Khamenei ya ce shugabannin ƙasashen yankin ya kamata su gano waɗanda ya kira “ainihin maƙiyansu” , su fahimci shirye-shiryensu da manufofinsu.

Ya ƙara da cewa Amurka da Isra’ila ba maƙiyan Iran da wasu ƙungiyoyin da ke adawa da su kaɗai ba ne, a cewarsa, suna kallon su a matsayin barazana ga sauran ƙasashen Musulmi na yankin Yammacin Asiya da Arewacin Afirka, har da waɗanda ke da alaƙa da su.

Saƙon ya zo ne watanni shida bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, waɗanda wasu majiyoyi na kusa da jami’an Iran suka ce sun yi sanadin mutuwar mahaifinsa, Ali Khamenei , tare da jikkata Mojtaba.

Wannan shi ne saƙo na biyu da Mojtaba Khamenei ya fitar a cikin 'yan kwanakin nan yana jaddada muhimmancin haɗin kai a cikin gida.

A wani saƙon da aka wallafa a ranar 28 ga Agusta , ya yi gargaɗi kan kalamai da ka iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Iran.