Rundunar Sojin Saman Najeriya ta fitar da sunayen mutum 25 da ta ce sun rasa rayukansu a hatsarin wani jirgin sama mai saukar ungulu da ya faru a jihar Ondo ranar Litinin.

Hukumomin tsaro sun ce jirgin na gudanar da wani aiki na yau da kullum daga Benin zuwa Legas, kafin ya faɗi kusa da wani sansanin sojojin ruwa a safiyar Litinin.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa jirgin ya faɗi ne kusa da wani kurmi, inda aka gano tufafi da takalma a wurin. Ya ce kuma ana iya ganin hayaki na tashi daga yankin.

Rahotannin farko sun nuna cewa mutum 32 ne suka mutu a hatsarin, sai dai daga baya Rundunar Sojin Sama ta tabbatar da mutuwar mutum 25.

Rundunar, ƙarƙashin jagorancin babban hafsanta, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ta fitar da sunayen waɗanda suka mutu a shafinta na X ranar Talata.

Mutanen sun haɗa da matuƙan jirgin biyar da fasinjoji 20. Rundunar ta ce babu wanda ya tsira daga hatsarin.

Matuƙa da ma'aikatan jirgin

  • Squadron Leader MI Aburime
  • Squadron Leader AP Man-Ugwueje
  • Flight Lieutenant IS Bako
  • Warrant Officer Abubakar A — mai gyaran jirgi
  • Corporal Uguru HC — mai gyaran jirgi

Fasinjoji

  • Flight Lieutenant TL Lazarus
  • Flight Lieutenant M Akinloye
  • Flying Officer IM Adeshina
  • Master Warrant Officer Onwuka F
  • Master Warrant Officer Matini BA
  • Warrant Officer Nuhu FS
  • Flight Sergeant James RB
  • Flight Sergeant Mohammed AI
  • Sergeant Ani AE
  • Sergeant Izibenikien SI
  • Sergeant Alafuka C
  • Sergeant Mbadugha AN
  • Lance Corporal Ugwuba FC
  • Lance Corporal Eledan GE
  • Mrs Ezeh Nneka
  • Godstmine Tarabina
  • Joy Micheal
  • Sunday Micheal
  • Ukeme David
  • Gideon Omotola