Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta nuna damuwa kan yadda wasu kamfanonin shirya tafiye-tafiyen Umrah ke ɗaukar hotuna da bidiyon masu ibada a ƙasa mai tsarki domin tallata ayyukansu.

Rahama Sadau ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce tana da sha’awar zuwa Umrah tare da jama’a, sai dai yadda wasu kamfanonin ke gudanar da harkokinsu na sanyaya mata gwiwa.

Jarumar ta ce ya kamata a mayar da Umrah kan ibada, maimakon a mayar da ita wata dama ta ɗaukar hotuna da bidiyoyin da za a wallafa a kafafen sada zumunta.

Saƙon nata ya jawo hankalin mutane da dama, ciki har da fitaccen malamin addinin Musulunci, Mufti Menk, wanda ya mayar da martani kan batun.

Mufti Menk ya kuma ba Rahama Sadau shawarar wani kamfani da za ta iya bi domin gudanar da Umrah, yana mai cewa kamfanin na bai wa mahajjata damar gudanar da ibadarsu cikin sirri.

Sai dai ya ce a wannan zamani, mutane da dama kan samu ƙwarin gwiwar zuwa Umrah ne bayan sun ga wasu sun je.

Duk da haka, ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da cewa ɗaukar hotuna ko bidiyo bai zama abin da aka fi mayar da hankali a kai ba yayin gudanar da ibadar.