Gwamnatin Tarayya ta ce nan ba da jimawa ba za ta kawo ƙarshen yanka dabbobi a wuraren da ba su da tsari a faɗin ƙasar, a wani ɓangare na ƙoƙarin zamanantar da masana’antar naman dabbobi da kokarin sanya najeriya tayi gogayya da kasuwanni nama na duniya.

Ministan Bunƙasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Kaduna, yayin ƙaddamar da sabon kamfanin samar da  aincin shanu na TruValue Cattle Feed na kamfanin Olam Agri, wanda ake amfani da shi wajen kiwon shanu don samar da nama da madara.

Maiha ya ce gwamnati ta riga ta fara gina dakunan yanka dabbobi na zamani, kuma za a buƙaci dabbobin da za a kai kasuwa su ratsa wuraren kiwo na musamman (feedlots) tare da cika ƙa’idojin da aka gindaya kafin a yanka su.

Ya ce, “Za mu ci gaba da wannan ƙoƙari domin tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za mu daina sayar da dabbobi masu rai, kuma duk dabbar da za a yanka a wannan ƙasa dole ne a yanka ta a cikin ingantaccen tsarin dakin yanka dabbobi na zamani.”

A cewarsa, gwamnati ta riga ta gudanar da bikin aza harsashin ginin dakunan yanka dabbobi guda biyu da kuma ƙaramin dakin yanka dabbobi guda ɗaya a yankin Offa, yayin da wani sabon wurin da ake ginawa a Abuja zai kasance yana da ƙarfin sarrafa bijimansa 1,000 da ƙananan dabbobi 3,000 a kowace rana.

Ya bayyana cewa samar da wuraren kiwo na musamman, dakunan yanka dabbobi na zamani, masana’antun sarrafa nama da kuma tsarin adana nama cikin sanyi (cold-chain) zai taimaka wa Najeriya wajen samar da nama mai inganci wanda za a iya bin diddigin tushensa, domin amfanin cikin gida da kuma fitar da shi zuwa ƙasashen waje.