Sakataren Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Olufemi Oke-Osanyintolu ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:56 na dare a ranar Alhamis, a agini mai  lamba 42, Governors Road, Aboru, dake ƙaramar hukumar Alimosho ta jihar.

Oke-Osanyintolu ya ce nan take aka tura ƙungiyar Alpha Eagle Response Team ta hukumar zuwa wurin bayan samun kiran neman agaji.

A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa ginin ya ruguje ne a lokacin da ake rushe shi da hannu.

Ya ƙara da cewa: “Bayan isowar jami’an agajin farko, sun tabbatar da cewa ginin ya ruguje ne yayin aikin rusau, inda ma’aikata suka makale a ƙarƙashin baraguzan ginin.”

Ya bayyana cewa hukumar ta kunna Tsarin Ba da Agajin Gaggawa na Jihar tare da ɗaukar nauyin aikin ceto, tana kuma haɗa gwiwa da sauran jami’an agajin gaggawa da ke wurin.