Gwamnatin Tarayya ta sanar da cire kuɗin data ga miliyoyin ɗaliban Najeriya da ke amfani da dandalin ilimi da aka amince da su, a wani gagarumin shiri na bunƙasa ilimin zamani ta hanyar fasahar zamani, da nufin sauƙaƙa wa ɗalibai samun kayan karatu a faɗin ƙasar.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ƙaddamar da shirin “Initiative for Zero-Rated Access to Educational Platforms and Content in Nigeria”, inda ya ce shirin zai taimaka wajen tabbatar da cewa tsadar data bazai hana matasan kasarnan smaun ingantatcen ilimi ba
Alausa ya ce shirin, wanda yake ƙarƙashin Renewed Hope Ajanda ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, an tsara shi ne domin kawo karshen matsalar data dake hana wasu daliba kasarnan samun kayayyakin karatu.
A cewars shirin nada manufar isar da karatu da saukaka shi ga dukan yara dake kasarnan, domin basu damar gogayya da takwarorinsu na duniya