Rundunar ‘yansandan Najeriya ta kama Hafsat Abubakar, mai shekara 27, bisa zargin ƙirƙira da yaɗa wata takardar bogi da ke cewa kamfanin OPay zai daina aiki.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Anietie Iniedu, ya bayyana cewa an kama Hafsat ne ranar 4 ga Satumba 2026, bayan OPay ta kai ƙorafi ga rundunar ‘yansanda a ranar 31 ga Agusta.
Ya ce cibiyar yaƙi da laifukan yanar gizo ta ‘yansanda ta gudanar da binciken ƙwaƙƙwafi na Internet, inda aka gano cewa takardar ta samo asali ne daga wani shafin X da Hafsat Abubakar ke amfani da shi.
‘Yansandan sun ce takardar ta bogi ce kuma an gabatar da ita tamkar sanarwar hukuma daga OPay, inda ta yi ikirarin cewa kamfanin zai dakatar da ayyukansa daga 1 ga Satumba.
OPay ya musanta sanarwar, yana mai cewa kamfanin na ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.
Rundunar ‘yansandan ta yi gargadin cewa yaɗa bayanan bogi ta kafafen sada zumunta na iya haifar da firgici, matsalar kuɗi da kuma ɓata sunan kamfanoni.
Ta kuma bukaci jama’a da su riƙa tabbatar da sahihancin muhimman bayanai daga majiyoyin hukuma kafin su yaɗa su.