Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan wani mutum mai suna Ibrahim Khalil Danshagamu, mazaunin unguwar Gaida da ke Karamar Hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Rundunar ta ce da misalin ƙarfe 11:30 na daren Litinin, 8 ga Satumba, 2026, ta samu rahoton gaggawa daga kwamandan kungiyar sa-kai ta Gaida cewa wasu ’yan daba da ba a san ko su waye ba sun kutsa cikin gidan marigayin da ƙarfi tare da kai masa hari da wasu abubuwa masu kaifi.
Bayan samun rahoton, jami’an sashen ’yan sanda na Kumbotso sun garzaya wurin da lamarin ya faru. An garzaya da wanda aka kai wa harin zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa bayan isarsa asibitin.
Haka zalika Rundunar ta ce bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, DPO na Kumbotso tare da jami’an rundunar ta musamman da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma sun gudanar da wani samame na musamman wanda ya kai ga kama mutane biyu da ake zargi da alaka da lamarin.
A halin yanzu, ana tsare da wadanda ake zargin domin gudanar da bincike da yi musu tambayoyi, yayin da rundunar ke ci gaba da kokarin cafke duk wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin.
Haka kuma, rundunar ta ce ana tattara bayanai da gudanar da binciken kwararru domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma dalilin kai harin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana damuwarsa kan lamarin tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Ya kuma jaddada cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gano, kama da gurfanar da duk wadanda aka samu da hannu a aikata laifukan tashin hankali, bisa tanadin doka.
Rundunar ta yabawa kungiyar sa-kai ta Gaida bisa samar da bayanan cikin gaggawa, wanda ta ce ya taimaka wajen kai daukin ’yan sanda cikin lokaci.
Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kasance cikin taka-tsantsan tare da ci gaba da bai wa ’yan sanda sahihan bayanai ta hanyar ofishin ’yan sanda mafi kusa ko lambobin gaggawa na rundunar.