Jami’ar Kimiyya da Fasaha Ta Aliko Dangote dake Wudil, ta karyata rahoton da ke cewa an samu jinkiri wajen tura wasu daga cikin ɗalibanta zuwa shirin yi wa ƙasa hidima na NYSC.
A cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Abdullahi Datti Abdullahi, ya fitar ranar 9 ga Satumba 2026, jami’ar ta ce babu ɗalibin da ya kammala karatu a watan Satumba 2025, domin a lokacin ne kawai suka kammala jarabawar shekarar ƙarshe. Ta ce sai an kammala tantance sakamako da sauran matakan amincewa kafin a tabbatar da kammala karatu.
Jami'ar Ta bayyana cewa ta tura ɗalibai 10,232 aikin NYSC tsakanin 2024 Batch A da 2026 Batch C, yayin da aka riga aka tura 1,763 a cikin 2026 Batch C. Jami’ar ta ce wasu dalibai na iya kasa samun damar zuwa NYSC saboda rashin cike bayanan NYSC, rashin tabbatar da shigar JAMB ko rashin bin umarnin aikin yi wa ƙasa hidima.
Jami’ar ta kuma bukaci iyaye, ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki da su riƙa neman bayanai daga hukumomin jami’ar da suka dace, tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa.