Hedikwatar Rundunar Sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM, ta mayar wa BBC martani kan ikirarin Iran na cewa ta kama wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku maras matuƙi na Amurka a mashigin Hormuz.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun CENTCOM, Laftanar Kyaftin Tim Hawkins, ya ce jirgin ruwan ƙarƙashin tekun ya lalace ne sama da kwana guda da ya gabata.

Ya ce jirgin yana sintiri ne a ruwan yankin domin tallafa wa ayyukan sojojin Amurka da ke gudana a yankin.

Hawkins ya bayyana cewa jirgin tsohon samfuri ne, kuma ba ya tattara muhimman bayanan sirri. Ya kuma ce ba ya ɗauke da na'urorin radar ko wasu na'urorin tattara bayanan sirri.

Ya ƙara da cewa ayyukan sojojin Amurka a ruwan yankin na ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

A baya, kamfanin dillancin labaran Fars, wanda ke da alaƙa da Rundunar Juyin Juya Halin Iran, IRGC, ya bayar da rahoton cewa Iran ta “kama” wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku maras matuƙi na Amurka mai amfani da fasahar zamani.

Fars ta yi iƙirarin cewa jirgin na daga cikin sabbin jiragen ruwa marasa matuƙi da sojojin Amurka ke amfani da su, kuma an kama shi ne a bakin mashigar Hormuz.

Sai dai bayanin CENTCOM ya ƙalubalanci wannan ikirari, inda Amurka ta ce jirgin ya lalace ne tun kafin lokacin da Iran ta ce ta kama shi.