Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin alamun nuna wariyar addini a shari'ar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

A wata sanarwa da Sakataren Janar na majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya fitar, NSCIA ta ce ta daɗe tana ƙaurace wa yin tsokaci kan shari'ar, domin tun farko ta ɗauke ta a matsayin shari'ar yau da kullum, tana mai fatan kotuna za su tabbatar da adalci.

Sai dai majalisar ta ce wasu abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun sa ta fara ganin akwai yiwuwar wariyar addini na taka rawa a shari'ar.

Wannan na zuwa ne bayan kalaman Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda ya zargi El-Rufai da hannu wajen shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamna.

NSCIA ta ce kalaman ministan sun sa ta sauya matsayinta na farko na kin tsoma baki, saboda tana ganin akwai alamun yiwuwar wani “son zuciya na wariyar addini” a kan tsohon gwamnan.

Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da bangaren shari'a da su tabbatar da cewa ba a amfani da hukumomin gwamnati ko tsarin shari'a wajen aiwatar da wata manufa ta bangaranci a kan El-Rufai.

Haka kuma, ta yi kira ga jama'a da su guji kalaman tunzura jama'a da za su iya yin tasiri kan shari'ar ko kuma ƙara dagula yanayin tsaro a Najeriya.