Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran, IRGC, ta yi iƙirarin cewa ta kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka guda biyu da makamai masu linzami.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a safiyar Laraba, ta ce rundunar ta kai harin ne kan jiragen DDG-119 da DDG-53, waɗanda ke ɗauke da makamai masu linzami da tsarin kariya na Aegis.
IRGC ta yi iƙirarin cewa makaman da ta harba sun yi wa jiragen ruwan babban lahani.
Sai dai rahotannin da suka fito daga ɓangaren Amurka sun ce jiragen ruwan Amurkan sun yi nasarar kauce wa hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai, ba tare da wani jami’in sojan Amurka ya ji rauni ba.
Hakan na zuwa ne bayan da Rundunar Tsakiyar Sojin Amurka, CENTCOM, ta sanar da lalata tankokin ɗanyen man Iran guda biyar a ranar Talata, a matsayin martani ga hare-haren makamai masu linzami da IRGC ta kai kan wani jirgin ruwan yaƙin Amurka.
Ci gaba da musayar hare-haren na ƙara tsananta rikicin tsakanin Iran da Amurka, tare da ƙara barazana ga tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa da jigilar makamashi a yankin mashigar Hormuz.