Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekaru 490 a gidan yari da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan Bankin Shige da Fitar da Kayayyaki na Najeriya (NEXIM Bank), Robert Orya.
Kotun ta same shi da laifi kan tuhume-tuhume 49, inda aka yanke masa hukuncin shekaru 10 a kan kowace tuhuma, wanda ya kai jimillar shekaru 490. Sai dai kotun ta bayyana cewa za a yi zaman gidan yarin a lokaci guda, ba ɗaya bayan ɗaya ba.
Orya ya shugabanci NEXIM Bank daga shekarar 2009 zuwa 2016. A lokacin da yake kan mukamin ne aka sake naɗa shi a shekarar 2014 a zamanin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.
Bayan barin mukaminsa, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta gurfanar da shi a gaban kotu a shekarar 2021, bisa tuhume-tuhume 49 da suka haɗa da zargin karɓar kuɗi ta hanyar yaudara da sauran laifukan da suka shafi kuɗaɗen da suka kai kimanin naira biliyan 2.4.
A ranar 5 ga Fabrairu, 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifi, tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 490.
A hukuncin da kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙara ya yanke, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muhammed Danjuma, kotun ta ce alkalin kotun farko, Mai Shari’a Messiri, ya yi daidai wajen yanke hukuncin.
Mai Shari’a Danjuma, tare da sauran alkalan biyu, Ntong Ntong da Ele Enenche, sun ce masu gabatar da ƙara sun samu nasarar tabbatar da tuhumar da ake yi wa Orya ba tare da wata tantama mai ma’ana ba.