Kamfanin dillancin labaran Fars na Iran, wanda ke da alaƙa da Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta ƙasar, IRGC, ya ce Iran ta ƙwace wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku na Amurka mai sarrafa kansa a mashigar Hormuz.

Rahoton ya ce jirgin na daga cikin sabbin jiragen ruwa marasa matuƙi masu amfani da fasahar zamani da sojojin Amurka ke da su.

Fars ta ce jami’an Iran sun kama jirgin ne a mashigar Hormuz, hanyar ruwa mai matuƙar muhimmanci da ke haɗa Tekun Fasha da Tekun Oman.

Sai dai har yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin Amurka da ta tabbatar da wannan ikirari ko bayyana abin da ya faru da jirgin.

Wannan na zuwa ne yayin da ake samun ƙarin tashin hankali tsakanin Iran da Amurka a yankin Tekun Fasha da mashigar Hormuz.