Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ya ce ƙasar na aiki tare da abokan hulɗarta a yankin da kuma wasu ƙasashen duniya, ciki har da China, domin ƙoƙarin sake fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.
A halin yanzu, Firaministan Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar ne ke jagorantar wata tawaga zuwa birnin Beijing na ƙasar China.
A cewar Iran, Pakistan ce ke taka rawa mafi girma wajen shiga tsakani tsakanin Tehran da Washington a halin yanzu, sai dai Qatar ma na taka muhimmiyar rawa wajen ƙoƙarin sasanta ɓangarorin biyu.
Rahotanni sun ce a kwanakin baya wata tawagar jami’an diflomasiyyar Qatar ta ziyarci Iran, inda ta gana da Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Abbas Araqchi.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce ziyarar ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin ci gaba da rage tashin hankali a yankin.
Qatar ta ce za ta ci gaba da yin amfani da hanyoyin diflomasiyya tare da ƙasashen da abin ya shafa domin samar da yanayin da zai ba da damar komawa kan teburin tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.