Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, ya yi kira ga ƙungiyar Hamas da ta mika makamanta tare da rusa abin da ya kira “ginshiƙan ayyukan ta’addanci” na ƙungiyar.
Miliband ya ce, a ƙarƙashin shirin zaman lafiya mai ɗauke da yarjejeniyoyi 20, Hamas ba za ta taka wata rawa a shugabancin Gaza a nan gaba ba.
Ya bayyana cewa Isra’ila na da haƙƙin rayuwa cikin tsaro ba tare da fargaba ba, amma ya ce sama da mutum 70,000 aka kashe a Gaza, ciki har da yara kusan 20,000.
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya ya kuma ce ana ci gaba da samun cikas wajen kai agajin jinƙai da kayan ceton rayuka zuwa Gaza.
Ya ƙara da cewa sama da kashi 60 cikin 100 na gidajen Gaza sun lalace ko kuma sun koma kufai sakamakon yaƙin da ake ci gaba da yi a yankin.