Gwamnatin Kenya ta bai wa baƙin haure da ke gudanar da ƙananan sana’o’i a ƙasar wa’adin kwanaki 90 su mallaki takardun zama, izinin aiki da kuma lasisin gudanar da kasuwanci.

Kakakin Fadar Shugaban Ƙasar, Hussein Mohammed, ya ce za a gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar ofisoshin jakadancin ƙasashen da abin ya shafa, domin bai wa baƙin hauren damar daidaita takardunsu da harkokin kasuwancinsu cikin tsari.

Ya ce gwamnati za ta yi amfani da kwanaki 90 masu zuwa wajen gudanar da aikin, kuma bayan cikar wa’adin za a fara tsaurara aiwatar da dokokin shige da fice.

Matakin ya biyo bayan umarnin Shugaban Ƙasar, William Ruto, na cewa ya kamata ’yan Kenya su riƙa gudanar da wasu ƙananan sana’o’i, ciki har da tallace-tallace a kan tituna da wasu sana’o’in sayar da kayayyaki.

Wannan mataki ya haifar da fargaba tsakanin wasu ’yan kasuwa ’yan ƙasashen waje, musamman ’yan ƙasar Burundi da ke gudanar da ƙananan sana’o’i a Kenya.

Sai dai gwamnatin Kenya ta ce matakin ba na tsoratar da baƙin haure ba ne, tana mai cewa manufarta ita ce tabbatar da cewa duk wanda ke gudanar da kasuwanci a ƙasar ya bi dokokin da suka shafi zama da kuma izinin aiki.