Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda ya gabatarwa majalisar dokokin jihar da daftarin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2027, wanda ya kai Naira biliyan 828.64 a ranar talata domin amincewa.
Kusan kashi 77 cikin 100 na kasafin kuɗin an ware shi ne domin ayyukan raya ƙasa.
Kasafin kuɗin mi taken “Building Your Future IV”, ya ware Naira biliyan 637.91, wato kashi 76.98 cikin 100, domin ayyukan manyan ayyuka, yayin da aka ware Naira biliyan 190.73, kwatankwacin kashi 23.02 cikin 100, domin gudanar da ayyukan yau da kullum na gwamnati.
Adadin kasafin kudin ya ragu da Naira biliyan 69.23 idan aka kwatanta da kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka amince da shi.
Gwamna Radda ya bayyana cewa raguwar ta samo asali ne daga wani sabon hasashe da gwamnati ta yi kan yadda ake sa ran samun kuɗaɗen shiga da kuma yadda za a kashe su.
Yayin da yake gabatar da kasafin kuɗin a gaban ’yan majalisar, Radda ya ce gwamnati ta bi tsarin “mai ma’ana, mai tsari da kuma na zahiri” wajen tsara kasafin kuɗin.