Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sake tunatar da maniyyatan Hajjin 2027 cewa ranar 26 ga Satumba ce wa’adin ƙarshe na kammala rajista da biyan kuɗin aikin Hajjin.
NAHCON ta yi wannan tunatarwa ne cikin saƙonnin da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, inda ta buƙaci maniyyatan da ba su kammala rajista ko biyan kuɗaɗen aikin Hajjin ba da su yi hakan kafin cikar wa’adin.
Hukumar ta ce wa’adin ya yi daidai da jadawalin da hukumomin Saudiyya suka gindaya domin shirye-shiryen aikin Hajjin 2027.
Ta ce kammala rajista da biyan kuɗaɗe cikin lokaci na da muhimmanci wajen daidaita bayanan maniyyata da kuma tsara rabon kujerun jiragen sama.
NAHCON ta kuma yi gargaɗin cewa rashin kammala waɗannan matakai kafin wa’adin na iya sa maniyyata su rasa guraben Hajjin da aka ware musu.
Hukumar ta buƙaci hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da kuma maniyyatan da kansu da su tabbatar sun kammala dukkan abubuwan da ake buƙata kafin lokacin Hajjin.
A watan Agusta, NAHCON ta sanar da kuɗaɗen aikin Hajjin 2027, inda maniyyatan da za su tashi daga Maiduguri da Yola za su biya Naira miliyan 7,560,822, yayin da maniyyatan yankin Arewa za su biya Naira miliyan 7,672,822.
Maniyyatan yankin Kudu kuwa za su biya Naira miliyan 7,882,822.