IHukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanya ranar 19 ga watan Satumba domin gudanar da zaɓukan cike gurbi guda biyar a jihohin Gombe, Kano, Bauchi da Delta.
Sakataren Yaɗa Labarai na Shugaban INEC, Tunde Oketola, ne ya tabbatar da hakan, inda ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN, cewa zaɓukan sun ƙunshi kujera guda ɗaya ta Majalisar Wakilai ta Tarayya da kuma kujerun majalisun jihohi guda huɗu.
A cewarsa, za a gudanar da zaɓen kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazabar Gombe/Kwami/Funakaye ta Jihar Gombe.
Yayin da zaɓukan kujerun majalisun jihohi za su gudana a mazabar Disina da Sakwa a Jihar Bauchi, Udu a Jihar Delta da Dawakin Kudu a Jihar Kano.
INEC ta ce shirye-shiryen gudanar da zaɓukan na ci gaba, domin tabbatar da sahihanci da gudanar da zaɓe cikin lumana a mazabun da abin ya shafa.