Wani bene mai hawa uku ya ruguje a yankin Wuse Zone 4 da ke Abuja, sa’o’i kaɗan bayan hukumomin kula da ci gaban birane sun rufe ginin tare da umartar mutanen da ke cikinsa su fice.

Hotuna da bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ginin ya ruguje, yayin da jama’a suka taru a wurin bayan faruwar lamarin.

Kawo yanzu ba a bayyana musabbabin rugujewar ginin ba.

Haka kuma, babu cikakken bayani kan ko akwai mutane a cikin ginin lokacin da ya ruguje, ko kuma ko akwai waɗanda tarkacen ginin ya danne.

Sai dai Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya ta ce ta samu kiran gaggawa game da rugujewar ginin da misalin ƙarfe 7:45 na daren Litinin.

Kakakin rundunar a Abuja, Josephine Adeh, ta ce an tura jami’an ’yan sanda zuwa wurin domin bayar da agajin gaggawa da kuma tabbatar da tsaron yankin.

Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin rugujewar da kuma tabbatar da ko akwai waɗanda abin ya shafa.