Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama mutum kusan 16 da ake zargi da hannu a wani rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a Ƙaramar Hukumar Dass.

Rundunar ta ce ana binciken waɗanda aka kama kan zargin haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da tarzoma da kuma kisan kai.

Kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya shaida wa BBC cewa binciken farko ya nuna cewa lamarin ya fara ne a ranar 4 ga Satumban 2026, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

Ya ce wani mutum mai suna Ibrahim El-Safwan, wanda aka fi sani da Jabala’i, ya haɗa baki da wasu mutane tare da kai wa wani mai tuka babur mai kafa uku, Abdulrahman Nuru, mai shekara 29, hari a yankin Tudun Wus da ke Dass.

A cewar SP Habib, waɗanda ake zargin sun tare Abdulrahman Nuru, wanda ke zaune a yankin Bundot na Dass, sannan suka yi masa mummunan sara da adda a sassa daban-daban na jikinsa.

Ya ce kisan ya haifar da tashin hankali a yankin, inda wasu fusatattun matasa suka taru ɗauke da adduna da wasu muggan makamai, suka nufi yankin da nufin ɗaukar fansa.

Kakakin ’yan sandan ya ce rundunar na ci gaba da ƙoƙarin cafke wasu daga cikin waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, waɗanda ake kyautata zaton sun tsere.

Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.