Iyalin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun bai wa Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya, wa’adin kwanaki bakwai da ya janye wasu zarge-zargen da ya yi wa tsohon gwamnan ko kuma su ɗauki matakin shari’a a kansa.

A wata sanarwa da ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai, ya fitar a madadin iyalan a ranar Litinin, ya ce Janar Musa ya yi zarge-zargen ne yayin wata hira kai tsaye da shirin Politics Today na Channels Television a ranar 3 ga Satumba.

Sanarwar ta ce ministan ya zargi El-Rufai da shirya kashe mutane a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamnan jihar.

Sai dai iyalan El-Rufai sun ce ministan bai gabatar da wata hujja da za ta tabbatar da wannan zargi ba.

Saboda haka, sun buƙaci Janar Musa da ya gabatar da hujjojin da ya dogara da su wajen yin kalaman, ko kuma ya janye su tare da ba da haƙuri a bainar jama’a, ta kafar da ya yi zargin.

A wata wasiƙa da lauyoyin El-Rufai suka aika wa ministan, sun ce irin waɗannan kalamai na iya sa a riƙa kallon tsohon gwamnan a matsayin wanda ya aikata kisan kai ko kuma ya ɗauki nauyin wasu ’yan bindiga.

Lauyoyin sun kuma buƙaci Janar Musa ya gabatar da dukkanin hujjoji, rahotanni da bayanan da ya dogara da su wajen yin zarge-zargen.

Baya ga haka, sun nemi ministan ya ɗauki alkawarin cewa ba zai sake maimaita ko yaɗa irin waɗannan kalamai ba, tare da biyan diyyar naira biliyan 10 saboda abin da suka bayyana a matsayin ɓata sunan El-Rufai.

Wasikar ta ce idan ba a samu amsa mai gamsarwa cikin wa’adin kwanaki bakwai ba, El-Rufai zai garzaya kotu domin neman ta ayyana kalaman a matsayin na ƙarya da kuma ɓata suna, tare da neman diyya da sauran matakan da doka ta tanada.