Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Alhaji Aminu Atiku a matsayin sabon Sarkin Zamfaran Zurmi, kuma Sarkin Masarautar Zurmi.
Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan shawarar masu zaɓen sarki na Masarautar Zurmi, bisa tanadin al’adu da dokokin jihar.
Alhaji Aminu Atiku, wanda ke riƙe da sarautar Dangaladiman Zurmi, shi ne zai zama Sarkin Zamfaran Zurmi na 21.
Ya maye gurbin marigayi Alhaji Bello Suleiman, wanda ya rasu a ranar 31 ga watan Agustan 2026.
Sabon sarkin ɗa ne ga marigayi Sarkin Zurmi na 19, Alhaji Atiku Abubakar.
A cikin saƙon taya murna, Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci sabon sarkin da ya yi koyi da magabatansa wajen gudanar da mulki bisa zaman lafiya, adalci da haɗin kai, tare da fifita walwalar al’ummar masarautarsa.
Gwamnan ya kuma buƙaci sarkin da ya ƙara ƙarfafa zaman lafiya tsakanin al’ummomin Masarautar Zurmi, tare da haɗa hannu da gwamnati da hukumomin tsaro domin inganta tsaro da bunƙasa ci gaban masarautar da jihar Zamfara baki ɗaya.