Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da dakile wani yunƙurin sace wasu mutane a yayin samamen da dakarunta suka kai kan ’yanbindiga a Jihar Zamfara.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Fansan Yamma, Kanal Aliyu Danja, ya ce an gudanar da ayyukan ne a ƙananan hukumomin Anka da Bungudu.

Kanal Danja ya ce binciken farko ya nuna cewa ’yanbindigar sun yi garkuwa da mutanen ne daga ƙaramar hukumar Gummi, inda suka shafe kusan makonni uku a hannun masu garkuwar kafin a ceto su.

Ya ce a halin yanzu waɗanda aka ceto suna samun kulawar lafiya da sauran tallafin da ya dace, kafin a miƙa su ga iyalansu.

A wani samame da aka kai a ƙaramar hukumar Bungudu kuma, rundunar ta ce ta dakile yunƙurin yin garkuwa da wasu mutane bayan da ’yanbindiga suka kai hari garin Dankurmi.

Rundunar ta ce dakarunta za su ci gaba da gudanar da ayyuka domin dakile ayyukan ’yanbindiga da kuma tabbatar da tsaron al’ummar yankin.