Sojojin Burkina Faso a ranar Laraba sun ce sun daƙile hare-haren da ƙungiyoyin ‘yanta’adda tare da kashe fiye da mahara 400
Sojojin Burkina Faso a ranar Laraba sun ce sun daƙile hare-haren da ƙungiyoyin ‘yanta’adda suka kai wasu sansanonin soji a ranar 30 ga Yuni, inda aka kashe fiye da mahara 400. Sojojin sun daƙile harin ne bayan samun taimako daga jiragen sama. A cikin wata sanarwa da Hedkwatar Sojin Burkina Faso ta fitar ranar Laraba da daddare, ta ce ‘yanta’addan sun kai hare-hare kan sansanonin soji da kuma jami’an sa-kai don kare ƙasa a ƙauyukan Gayeri da ke yankin Sirba, da Solhan da Sebba a yankin Liptako. A cewar rundunar, sojojin ƙasa, tare da goyon bayan jiragen sama, sun mayar da martani nan-take ga ha
