Jami'an tsaro a Afirka ta Kudu sun bayyana cewa an kama kusan mutum 900 bayan zanga-zangar da aka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewar hukumomi, an kama mafi yawan mutanen ne bisa zargin laifukan da suka haɗa da karya dokokin shige da fice da wasu laifuka, yayin da aka ce yawancin zanga-zangar ta gudana cikin lumana.

Sai dai wasu daga cikin gangamin sun rikide zuwa tashin hankali, lamarin da ya sa aka ƙara matakan tsaro a wasu yankuna.

Shugaban ƙasar, Cyril Ramaphosa , ya ce gwamnati na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki, tare da kira ga jama'a da su kiyaye doka da oda.