Tarihin Kafuwar Rundunar Sojin Najeriya: Daga Hausawa 18 Zuwa Ɗaya Daga Cikin Manyan Rundunonin Afirka
Rundunar Sojin Najeriya tana da dogon tarihi wanda ya samo asali tun zamanin mulkin mallakar Birtaniya. Abin mamaki, kafuwar rundunar ta fara ne da wasu Hausawa 18 da aka tara a Legas a shekarar 1863, kafin daga bisani ta zama ɗaya daga cikin manyan rundunonin soja mafi ƙarfi a nahiyar Afirka. Farkon Kafuwar Rundunar A shekarar 1863, Laftanar John Hawley Glover na Rundunar Sojin Ruwa ta Birtaniya (Royal Navy), wanda daga baya ya zama Gwamnan Mulkin Mallaka na Legas, ya ɗauki Hausawa 18 da ke zaune a Legas ya kafa wata ƙaramar runduna da ya sanya wa suna "Glover Hausas." An kafa rundunar ne dom
