top stories
Muhammad Ya Sake Zama Sunan Da Aka Fi Sanya Wa Jarirai A Ingila Da Wales
Sunan Muhammad ya sake zama sunan da iyaye suka fi sanya wa jariran maza a Ingila da Wales a shekarar 2025. Hukumar Ƙididdiga ta Birtaniya (Office for National Statistics) ce ta bayyana hakan a cikin rahoton shekara-shekara da ta fitar a ranar Alhamis kan sunayen da aka fi sanya wa jarirai a Ingila da Wales. Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne karo na uku a jere da sunan Muhammad ke zama mafi shahara a tsakanin sunayen jariran maza, bayan ya jagoranci jerin sunayen a shekarun 2023, 2024 da kuma 2025. Sakamakon ya nuna ci gaba da karuwar shaharar sunan Muhammad a Ingila da Wales, inda ya ci gaba
azubairu (legacy byline) · 10 Yul, 2026, 16:42
Sunan Muhammad ya sake zama sunan da iyaye suka fi sanya wa jariran maza a Ingila da Wales a shekarar 2025.
Hukumar Ƙididdiga ta Birtaniya (Office for National Statistics) ce ta bayyana hakan a cikin rahoton shekara-shekara da ta fitar a ranar Alhamis kan sunayen da aka fi sanya wa jarirai a Ingila da Wales.
Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne karo na uku a jere da sunan Muhammad ke zama mafi shahara a tsakanin sunayen jariran maza, bayan ya jagoranci jerin sunayen a shekarun 2023, 2024 da kuma 2025.
Sakamakon ya nuna ci gaba da karuwar shaharar sunan Muhammad a Ingila da Wales, inda ya ci gaba da kasancewa a sahun gaba wajen sunayen da iyaye ke zaɓa wa 'ya'yansu maza.