Amurka ta kai hare-hare Kan cibiyoyin nukiliya da ake ginawa a kudu maso yammacin Iran
Ƙungiyar makamashin nukiliya ta Iran ta sanar da cewa Amurka ta kai hari kan wani sansanin nukiliya da ake ginawa a kudu maso yammacin kasar a yau Lahadi. Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama kan Iran a yau lahadi don ɗaukar fansar mutuwar sojoji biyu a hare-haren da ta kai a Jordan, yayin da Tehran ke ci gaba da kai hari kan maƙwabtanta, ƙawayen Washington. Amurka ta bayyana cewa tana da niyyar ɗaukar fansa bayan mutuwar sojojinta biyu a hare-haren da Iran ta kai a Jordan a ranar Juma'a. Waɗannan su ne mutuwar Amurkawa ta farko tun bayan sake yaƙin a ranar 7 ga Yuli. Wani soja ya ɓa
