Ana sa ran shugaban Amurka, Donald Trump , zai halarci wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya tsakanin Spain da Argentina a ranar Lahadi, inda ake sa ran zai miƙa kofin ga tawagar da za ta lashe gasar tare da shugaban FIFA , Gianni Infantino .
Ziyarar Trump na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da ya janyo sakamakon wani rahoto da ya ce ya kira shugaban FIFA kai tsaye domin neman a ɗage dakatarwar ɗan wasan Amurka, Folarin Balogun , kafin wasan zagaye na 16.
Rahoton ya haifar da muhawara da suka daga wasu ɓangarori, waɗanda suka nuna damuwa kan yiwuwar tsoma bakin siyasa a harkokin ƙwallon ƙafa da FIFA ke gudanarwa.
Sai dai Trump ya bayyana cewa Gasar Kofin Duniya ta 2026 na ɗaya daga cikin gasannin da suka fi samun nasara a tarihi, yana mai cewa ta ƙara bunƙasa da kuma yaɗa farin jinin wasan ƙwallon ƙafa a Amurka.
Har zuwa yanzu, FIFA ba ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da rahoton cewa an nemi a sauya hukuncin dakatar da ɗan wasan ba.
