Farashin Danyen Mai Ya Sauka Bayan Dakatar Da Hare-Haren Amurka Da Iran
Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya ragu zuwa kusan dala 90 kan kowace ganga , bayan da Amurka da Iran suka dakatar da hare-haren da suke kai wa juna domin bai wa tattaunawar diflomasiyya damar ci gaba. A ranar Litinin, farashin Brent Crude ya ragu da kashi 6.76% zuwa dala 90.24 kan kowace ganga, yayin da US West Texas Intermediate (WTI) ya fadi da kashi 6.04% zuwa dala 83.92 kan kowace ganga. Rahotanni sun ce faduwar farashin ta biyo bayan dakatar da hare-haren da ɓangarorin biyu suka yi a ƙarshen mako, bayan kusan makonni biyu ana musayar hare-hare. Jakadan Amurka a Majalisar Ɗinkin D
