FIFA Ta Musanta Zargin Cewa UEFA Ta Biya wata Mata a lokacin da Gianni Infantino yake jagorantar hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA , ta musanta wani rahoto da ke zargin cewa UEFA ta biya wata mata da aka bayyana a matsayin masoyiyar shugabanta, Gianni Infantino , a lokacin da yake jagorantar hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai. Wani mai magana da yawun FIFA ya bayyana zargin da jaridar Daily Telegraph ta Birtaniya ta wallafa a matsayin wanda ba shi da wata gaskiya ko kaɗan , yana mai cewa Infantino ya yi kakkausar suka ga rahoton. Sai dai UEFA ta tabbatar da cewa ta biya matar da ake magana a kanta wani kuɗin sallama bayan ta bar aikinta, sannan ta ɗauki nauyin karatun MBA ɗinta. UEFA ta ce
