Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wani tsohon jami'inta, Nwaogu Ihechimere Ezeakolam , a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin kasancewa mamba a haramtacciyar ƙungiyar IPOB (Indigenous People of Biafra) .

An gurfanar da shi ne a ranar Alhamis a gaban Mai Shari'a Mohammed Garba Umar kan tuhume-tuhume guda huɗu da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kansa.

DSS na zargin Ezeakolam da bai wa IPOB goyon baya ta hanyar samar mata da kayan aiki, shiga ƙungiyar duk da sanin cewa an haramta ayyukanta, da kuma wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta domin ƙarfafa jama'a su mara mata baya.

Hukumar ta ce waɗannan ayyuka sun saɓa wa tanade-tanaden Dokar Yaƙi da Ta'addanci ta 2022 .

Sai dai bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Ezeakolam ya musanta aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da su.

Mai Shari'a Mohammed Garba Umar ya ɗage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa 29 ga Oktoba , domin fara sauraron ƙarar, sannan ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a Gidan Gyaran Hali na Kuje har sai an yanke hukunci kan buƙatar belinsa.

A shekarar 2017, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana IPOB a matsayin ƙungiyar ta'addanci tare da haramta dukkan ayyukanta a faɗin ƙasar.