AMMASCO RADIO NEWSROOM

Labarai

Gwamna Abba Ya Amince da Ƙarin Albashin Malaman Jami’o’in Kano

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf , ya amince da ƙarin albashi ga malamai da sauran ma’aikatan jami’o’in jihar. Ƙarin albashin zai shafi Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da kuma Jami’ar Northwest . Gwamnan ya amince da matakin ne bayan wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta kafa ya duba buƙatar jami’o’in biyu na shigar da sabon tsarin albashin cikin tsarin jihar. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa , ya fitar ranar Litinin, sabon tsarin albashin ya fara aiki tun daga Janairun 2026 , yayin da za a fara biyan ƙarin kuɗin daga

NERC Ta Rushe Kwamitin Gudanarwar Kaduna Electric

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NERC , ta rushe kwamitin gudanarwar kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna Electric , sakamakon matsalar kuɗi da kuma gazawar kamfanin wajen cika wasu muhimman sharuɗɗa. NERC ta ce matakin ya fara aiki ne daga ranar 10 ga Agustan 2026 , bisa tanade-tanaden sashe na 75 zuwa 79 na Dokar Wutar Lantarki ta 2023 . Hukumar ta bayyana cewa Kaduna Electric ya tara bashin sama da naira biliyan 118.6 na wutar lantarki a watan Mayun 2026, wanda ya sa jimillar bashin kamfanin ya kai kusan naira biliyan 456.5 . NERC ta ce a shekarar 2025, kamfanin ya biya kash

Sojoji Sun Ceto Mutane 33 da ’Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Su a Zamfara

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 33 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara. Rundunar ta ce ta samu sahihan bayanai kan sace fasinjojin ne yayin da suke tafiya a yankin Magazu , inda dakarunta tare da ’yan sandan Tsafe suka fara aikin ceto. A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja , ya fitar, ya ce jami’an tsaron sun samu labarin lamarin ne da yammacin ranar 8 ga Agusta, 2026 . Ya ce nan take dakarun suka nufi wurin, inda suka yi arangama da ’yan bindigar yayin da

Kashim Shettima Zai Shafe Mako Biyu Yana Karatu da Nazari a Lokacin Hutu

Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima , zai shafe makonni biyu yana karatu da yin nazari kan rayuwa da harkokin shugabanci yayin hutunsa na makonni biyu. Mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha , ya bayyana cewa hutun zai ba Shettima damar zurfafa ilimi da kuma yin tunani kan muhimman batutuwan da suka shafi aikinsa da hidimarsa ga Najeriya. Ya ce Shettima ya saba amfani da irin wannan lokaci wajen karatu, nazari da koyon sabbin abubuwa, yana mai cewa shugabanci mai ɗorewa na buƙatar mutum ya ci gaba da neman ilimi a kowane lokaci. Nkwocha ya ƙara da cewa nisantar ayyukan yau da kullum

Shari’ar Kisan Tupac Shakur Za Ta Fara Bayan Shekaru 30

Batun kisan shahararren mawakin rap, Tupac Shakur , wanda ya kwashe kusan shekaru 30 ba a warware shi ba, yanzu ya shiga matakin shari’a, yayin da mutumin da ake zargi da hannu a kisan nasa zai gurfana a gaban kotu a Las Vegas. Duane “Keffe D” Davis , mai shekara 63, na fuskantar tuhuma guda ɗaya ta kisan kai da makami mai hatsari, da zargin aikata laifin domin inganta, ci gaba ko taimaka wa wata ƙungiyar masu aikata laifuka, dangane da mutuwar Shakur. Zaɓen alkalan kotun zai fara ne ranar Litinin, yayin da ake sa ran shari’ar za ta ɗauki kusan wata guda. Shari’ar za ta sake buɗe ɗaya daga cik

Matar Gwamnan Jihar Osun ta jagoranci zanga-zangar Mata kan tashe -tashen hankula da kamen Yan jam'iyarsu gabanin zaben Gwamnan jihar

Uwargidan Gwamnan Jihar Osun, Titilola Adeleke, ta jagoranci zanga-zangar mata a jihar domin nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin kame-kame ba tare da ka’ida ba da kuma tashin hankula, gabanin zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar. Matan, wadanda suka fito daga kungiyoyin ’yan kasuwa da masu sana’o’i daban-daban, sun yi tattaki daga hanyar Osogbo zuwa Ilobu, inda suka nufi hedikwatar rundunar ’yansandan jihar da ke Osogbo. Adeleke ta bukaci ’yansanda su gudanar da bincike kan wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da take zargi da hannu wajen tashin hankulan da ake samu a jihar. Ta

Yan sanda a Jihar kwara sun kama wata mata da ake zargin da kashe yar kishiyarta

Rundunar ’yan sandan Jihar Kwara ta kama wata mata mai suna Sadiat Yunusa, bisa zargin ta shake ’yar mijinta mai shekaru uku, Ummaiyat har ta mutu a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar. A cewar ’yan sandan, wadda ake zargin ta bayyana cewa mijinta ya yi watsi da ita da ’ya’yanta uku, tare da fifta kishiyarta da yar ta ta. ’Yan sandan sun ce wadda ake zargin ta yaudari yarinyar ne har ta ja ta zuwa cikin gonaki da ke kusa, inda ake zargin ta kashe ta bayan wata doguwar takaddamar. Da take ƙarin bayani kan lamarin, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta rundunar ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta c

kuɗin hayar gida mai ɗakuna biyu a wasu manyan unguwannin Lagos Island ya yi matuƙar tashin gwauron zabi, inda ya kai Naira miliyan 17.25

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa kuɗin hayar gida mai ɗakuna biyu a wasu manyan unguwannin Lagos Island ya yi matuƙar tashin gwauron zabi, inda ya kai Naira miliyan 17.25 Rahoton Lagos Island Residential Market Report 2026 ya nuna cewa farashin haya ya ƙaru sosai a tsakanin shekarar 2022 zuwa 2026 a Ikoyi, Victoria Island, Lekki Phase 1 da Ikate. A Ikoyi, matsakaicin kuɗin hayar gida mai ɗakuna biyu ya kai Naira miliyan 17.25 a shekara, daga Naira miliyan 8 a shekarar 2022. Victoria Island ce ke biye da Ikoyi, inda hayar gida mai ɗakuna biyu ta kai Naira miliyan 15 a shekara, daga Naira miliy

Tinubu ya buƙaci shugabannin addinai su yi Allah-wadai da ta’addanci da garkuwa da mutane

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci shugabannin addinai da su ci gaba da yin magana a fili kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga, da kuma amfani da addini wajen haifar da fitina tsakanin al'umma. Tinubu ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Kano, cikin saƙon fatan alheri da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya isar a madadinsa a wajen babban Mauludin Sheikh Ahmad Al-Tijani. A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Yomi Odunuga, ya fitar, shugaban ya bayyana cewa shugabannin addinai na da muhimmiyar rawa wajen tunkarar tashin hankali,

Za a dawo cigaba da gudanar da shirin rigakafin cizon sauro ranar Laraba, 12 ga Agusta 2026 bayan Rahoton Kwamitin bincike da gwamnatin kano ta nada

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara ƙarfafa sa-ido kan tsarin gudanar da shirin rigakafin maganin cizon sauro na Seasonal Malaria Chemoprevention (SMC) na shekarar 2026, bayan kammala wani cikakken bita kan matakan gudanar da shirin, takardun bayanai da kuma tsarin ma’aikatan da za su aiwatar da shi a faɗin jihar. Wannan na cikin wata Sanarwa mai dauke da sa hannun jami'ar yada labarai ta hukumar Lafiya a matakin farko Sa'adatu Suleiman A cewar sanarwar, mataki ya biyo bayan kafa wani kwamitin bincike da Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya yi a ranar Laraba, 5 ga Agusta 2026, domin gudanar da bincik

NDLEA ta cafke hodar iblis da aka ɓoye cikin cajar waya zuwa Saudiyya

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce jami’anta sun cafke wani kayan hodar iblis (cocaine) da aka ɓoye cikin cajar wayoyi, wanda ake safararsa zuwa ƙasar Saudiyya. Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya yi gargadin cewa masu safarar miyagun kwayoyi na ƙara amfani da abubuwan yau da kullum wajen ɓoye miyagun ƙwayoyi domin guje wa kamun jami’an tsaro. Babafemi ya ce duk da cewa kayan sun yi kama da cajar wayoyi na yau da kullum, jami’an NDLEA ba su yaudare ba, domin bincike

INEC ta tsawaita wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan takarar Gwamna da na Majalisun Jihohi da zasu fafata a zaben 2027

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta tsawaita wa’adin miƙa sunayen ’yan takarar kujerar gwamna da na Majalisun Dokokin Jihohi da za su fafata a babban zaɓen ƙasa na Fabrairu 2027. Wa’adin miƙa sunayen ’yan takarar, wanda bisa sabon jadawalin zaɓe aka tsara zai ƙare ranar Asabar, 8 ga Agusta 2026, yanzu an tsawaita shi zuwa ranar Talata, 11 ga Agusta 2026. Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon buƙatun da jam’iyyun siyasa suka gabatar na neman ƙarin lokaci domin kammala aikin miƙa sunayen ’yan takararsu. A wani ci gaba, INEC ta sanar da masu kaɗa ƙuri’a da suka nemi sauya k

SERAP ta bukaci ‘yan takarar shugaban ƙasa 19 su bayyana kadarorinsu kafin zaɓen 202

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci dukkan ‘yan takarar shugaban ƙasa 19 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta sanar sunayensu, da su bayyana cikakkun bayanan kadarorinsu da basussukan da ake binsi, da na iyalansu sannan kuma, da na ‘ya’yansu da ba su kai shekara 18 ba, gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027. SERAP ta kuma buƙaci ‘yan takarar da su bayyana halastattun hanyoyin da suka samo manyan kadarorin da suke da su, tare da barranta mansu da sayen ƙuri’u da kuma bada cin hanci a Lokacin zaɓe. Ƙungiyar, a cikin wata sanarwa da Mataimakin Daraktanta, Kolawole Oluwadare, ya fitar, ta ce ta yi wa

DSS Ta Gurfanar da Tsohon Jami’inta Bisa Zargin Alaƙa da IPOB

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) ta gurfanar da wani tsohon jami’inta, Nwaogu Ihechimere Ezeakolam , a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa zargin kasancewa mamba a ƙungiyar IPOB da gwamnatin Najeriya ta haramta. An gurfanar da Ezeakolam ne ranar Alhamis a gaban Mai Shari’a Mohammed Garba Umar , kan tuhume-tuhume guda huɗu da gwamnatin tarayya ta shigar. DSS na zargin tsohon jami’in da bai wa IPOB goyon baya da kayan aiki, da kasancewa mamba a ƙungiyar duk da sanin cewa an haramta ta, da kuma wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta domin ƙarfafa mutane su mara wa ƙungiyar bay

Tinubu Ya Buƙaci Jami’o’i Su Fara Koyar da Kasuwar Hannayen Jari

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu , ya ce ya kamata jami’o’in ƙasar su fara koyar da ilimin kasuwar hannayen jari (Stock Market) domin bai wa matasa ƙarin ilimi da hanyoyin samar da arziki. A cewar Tinubu, koyar da wannan fanni a jami’o’i zai taimaka wajen wayar da kan matasa game da yadda kasuwar hannayen jari ke aiki, da kuma yadda za su iya amfani da ita wajen gina jari da samar da makomar tattalin arzikinsu . Ya ce ƙarin ilimi kan harkokin zuba jari zai taimaka wajen shirya matasa domin su kasance masu fahimtar damar da ke cikin kasuwannin kuɗi da kuma yadda za su iya taka rawa wajen bu

ICPC Ta Ce Ba Ta Samu Hujjar Laifi Kan Femi Gbajabiamila ba

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce ba ta samu wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila , ya aikata laifi a cikin badaƙalar wata hukumar gwamnati ta bogi ba. Hukumar ta bayyana cewa mutumin da ya yi iƙirarin kasancewa Darakta-Janar na Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC) , Prince Adeniyi Adeyemi, ba gwamnatin tarayya ta naɗa shi ba, kuma takardar naɗin da ya gabatar an gano cewa jabun takarda ce . ICPC ta kuma ce hukumar da Adeyemi ke ikirarin jagoranta ba a taɓa kafa ta ta hanyar wata doka ko umarnin gwamnati ba.

Mahaifin Lionel Messi, Jorge, Ya Rasu Yana da Shekara 68

Jorge Messi, mahaifin fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Argentina, Lionel Messi, ya rasu yana da shekara 68 bayan fama da rashin lafiya na dogon lokaci. Jorge, wanda ya kasance wakilin ɗansa tun lokacin da Messi yake da shekara 14, ya rasu a wani asibiti da ke garinsu na Rosario, Argentina, da sanyin safiyar Asabar. A lokacin gasar cin kofin duniya ta 2022, an samu rahotanni kan matsalar lafiyar Jorge, inda iyalan Messi suka tabbatar da cewa yana fama da “wani yanayin rashin lafiya” , amma ba su bayyana irin cutar da yake fama da ita ba. Jorge Messi ya taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ɗa

An Rantsar da Sabon Shugaban Colombia, Ya Sha Alwashin Yaƙar Masu Fataucin Miyagun Ƙwayoyi

An rantsar da sabon shugaban ƙasar Colombia, Abelardo de la Espriella , inda ya sha alwashin murƙushe abin da ya kira ta’addancin ƙungiyoyin masu fataucin miyagun ƙwayoyi. An gudanar da bikin rantsar da shi ne a birnin Cali , maimakon babban birnin ƙasar, Bogotá, matakin da ke nuni da mayar da hankali wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke aiki a yankin. Wakilin BBC ya ruwaito cewa, bayan rantsar da shi, shugaban ya gabatar da jawabi ga dakarun sojin ƙasar a wani sansani, inda ya buƙace su da su tabbatar da doka da ’yancin jama’a a Colombia. Gwamnatin Donald Trump ta nuna goyon b

An Naɗa Sheikh Abdulƙadir Jiyali Sarkin Takutaha na Ƙasar Hausa

An naɗa Sheikh Abdulƙadir Jiyali a matsayin Sarkin Takutaha na Ƙasar Hausa , a wani biki da aka gudanar a Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar , ranar Alhamis 6 ga Agusta 2026. Bikin naɗin ya samu halartar malamai, shugabanni da ɗimbin masoya Manzon Allah ﷺ, waɗanda suka bayyana farin cikinsu da wannan karramawa. A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Daura ya ce an yi naɗin ne bisa la’akari da gudummawar Sheikh Abdulƙadir Jiyali wajen cusa son Manzon Allah ﷺ a zukatan al’ummar Musulmi da ƙarfafa bin koyarwarsa . Ya kuma bayyana fatan cewa wannan sarauta za ta kasance alheri ga al’u

’Yan Majalisar Wakilai Sun Dakatar da Hutun Majalisa

Wasu ’yan Majalisar Wakilan Najeriya sun buƙaci majalisar tarayya ta dakatar da hutun da take yi, domin gudanar da zaman gaggawa kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa. ’Yan majalisar, waɗanda suka fito daga jam’iyyu daban-daban, sun kafa wata ƙungiya mai suna Save Democracy Group , wadda ta ce manufarta ita ce kare dimokuradiyya da ƙarfafa tsarin mulkin ƙasa. Ƙungiyar ta buƙaci shugabannin majalisun tarayya guda biyu da su kira zaman gaggawa domin tattauna yadda ake aiwatar da kasafin kuɗin shekarun 2024, 2025 da 2026 , tare da duba wasu batutuwa da suka shafi tafiyar da hark